Isa ga babban shafi
CANADA

Canada ta gurfanar da maharin masallacin Quebec

Hukumomin kasar Canada sun gurfanar da wani dalibi da ke da ra’ayin rikau a kotu don tuhumar sa da laifin kisan kai sakamakon bude wuta kan mai uwa da wabi a wani masallachin Quebec, in da mutane shida suka mutu.

Alexandre Bissonette da aka gurfanar saboda harin da ya kai a masallacin Quebec na Canada
Alexandre Bissonette da aka gurfanar saboda harin da ya kai a masallacin Quebec na Canada vdare.com
Talla

Wanda ake zargin Alexandre Bissonnette ya gurfana a gaban kotu ne bayan ya gabatar da kansa ga  jami'an 'yan sanda a matsayin wanda ya shirya kai harin.

Kakakin 'yan sandan Canada ta ce, sun samu izinin gudanar da bincike kuma suna fatar ganin sun samu shaidun da za su tabbatar musu da harin a matsayin na ta’addanci.

Ya zuwa yanzu dai jami’an tsaron ba su yi bayani kan dalilin da ya haifar da harin ba, yayin da Firaministan kasar Justin Treadeau ya bayyana harin a matsayin na ta’addancin da aka kaiwa al’ummar Musulmi a kasar.

Kafofin yada labaran Canada sun bayyana wanda ake zargin a matsayin wanda ya nuna sha’awarsa ga shugaban Amurka a Facebook da kuma goyan bayan Marine Le Pen, yar siyasar Faransa mai ra’ayin rikau.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.