Isa ga babban shafi
Chile

Wutar daji ta kona kauyuka a Chile

Kasashen Duniya na ci gaba da kai dauki ga al’ummar kasar Chile domin kashe wata wutar daji da yanzu haka ta kona kauyuka da gonaki da dama tare da hallaka mutane 10 .

An danganta wutar dajin a Chile a matsayin mafi muni da aka taba gani a duniya
An danganta wutar dajin a Chile a matsayin mafi muni da aka taba gani a duniya REUTERS
Talla

Shugabar kasar Michelle Bachelet ta bada umurnin bayar da wasu kudade na musamman don amfani da su wajen kashe wutar wadda tuni ta tilastawa mutane sama da 4,000 barin gidajen su.

Yanzu haka masu aikin kashe gobara sama da 4,000 ke yakar wutar da ya zuwa yanzu ta lashe eka kusan 700.

Akwai masu aikin kashe gobara guda hudu da ‘Yan sanda biyu cikin wadanda suka mutu.

Hasashen yanayi ya nuna wutar za ta ci gaba da ci saboda yanyin zafi da iska a yankin tsakiyar Chile da aka samu wutar dajin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.