Isa ga babban shafi
Amurka

“Mexico ba za ta biya kudaden gina Katanga ba”

Shugaban Kasar Mexico Enrique Pena Nieto ya yi allawadai da shirin shugaban Amurka Donald Trump na gina Katanga tsakanin kasashen biyu kamar yadda ya bayar da umurni.

Shugaban Mexico Enrique Pena Nieto
Shugaban Mexico Enrique Pena Nieto REUTERS/Carlos Jasso
Talla

A jawabin da ya yi wa al’ummar kasar, shugaba Nieto ya ce Mexico na bukatar a mutuntata a matsayin kasa mai ‘yanci.

Shugaban ya ce Mexico ba za ta biya sisin kwabo ba ga aikin gina katangar da Trump ya ce ita za ta biya.

Shugaban wanda bai ce komai da shirin ganawar da za su yi da Trump a makon gobe ba, ya ce ya bukaci ofisoshin Jakadancin kasar 50 da ke Amurka da su tashi tsaye domin kare muradun ‘yan kasar da ke zama a Amurka.

Tuni Shugaban Amurka Donald Trump ya bayar da umurnin fara aikin gina Katangar da za ta raba Amurka da Mexico, matakin da ya harzuka sauran shugabannin Yankin.

Trump ya bukaci jami’ansa su tsara yadda za’a fara ginin, inda yake cewa daga yau Amurka ta kama hanyar kare iyakokinta.

Yanzu haka kuma Shugaban Mexico Enrique Pena Nieto na fuskantar matsin lamba kan ya soke ganawar da zai yi da shugaban Amurka Donald Trump a makon gobe, domin nuna adawa da matakin gina katanga tsakanin iyakokin biyu.

Shugaban ya ce zai jira ya ji daga manyan jami’an da ya tura Amurka tare da tuntubar gwamnoni da ‘Yan majalisu kafin ya yanke shawarar watsi da goron gayyatar Donald Trump.

Gina katangar dai zai takaita kwararar ‘Yan Mexico zuwa Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.