Isa ga babban shafi
Amurka

CIA na binciken wani Jami’in Trump akan Rasha

Rahotanni daga  Amurka na cewar Hukumar leken asirin kasar na gudanar da bincike kan wani mai bai wa shugaba Donald Trump shawara game musayar bayanan da ya yi da wasu jami’an gwamnatin Rasha.

Michael Flynn mai ba shugaba Donald Trump shawara
Michael Flynn mai ba shugaba Donald Trump shawara ©REUTERS/Mike Segar
Talla

Jaridar Wall Street Journal ta ce ana binciken ne kan Janar Micharl Flynn, daya daga cikin masu bada shawara ga shugaba Trump da aka rantsar jiya Lahadi.

Binciken ya nuna cewar Janar Flynn mai ritaya ya karbi wasu kudade inda ya halarci wani biki a Moscow, tare da zaunawa teburi guda da shugaba Vladimir Putin.

Bayanan sun ce, tsohon sojan ya yi ta waya da Jakadan Rasha a Amurka, Sergey Kislyak, kwana guda kafin Obama ya bayyana daukar mataki kan Rasha.

Sai dai kuma kakakin Trump Sean Spicer ya musanta zargin inda ya ce Flynn ya zanta ne da jekadan na Rasha a ranar Kirsimeti kuma sun yi musayar sakwannin murnar sabuwar shekara ne ta wayar hannu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.