Isa ga babban shafi
Syria

Ana taron sasanta rikicin Syria a Kazakhstan

An bude taron sasanta rikicin Syria tsakanin wakilan gwamnati da ‘yan tawaye a birnin Astana na Kazakhstan da nufin karfafa yarjejeniyar tsagaita bude wuta da za ta kai ga magance rikicin kasar da aka shafe shekaru shida ana zubar da jini.

'Yan tawayen Syria za su yi tattaunawar keke da keke da wakilan gwamnatin Assad
'Yan tawayen Syria za su yi tattaunawar keke da keke da wakilan gwamnatin Assad REUTERS/Abdalrhman Ismail
Talla

Rasha da Iran da ke goyon bayan gwamnatin Assad da Turkiya da ke marawa ‘Yan tawaye da kuma Majalisar Dinkin Duniya ke jagorantar tattaunawar.

Rasha da Turkiya sun amince a yi tattaunawar ta keke da keke tsakanin wakilan ‘Yan tawaye da kuma na gwamnatin Bashar Al Assad wacce za ta kasance ta farko a tsakanin bangarorin biyu.

Sai dai kuma kakakin ‘Yan tawayen Yehya al Aridi ya ce a ranar farkon bude taron ba za su amince a yi tattaunawar ta keke da keke ba tsakaninsu da gwamnati.

‘Yan tawayen na son gwamnati ta mutunta yarjejeniyar tsagaita bude wuta a fadin Syria da aka amince a watan Disemba kafin su hau teburin tattaunawa da wakilan gwamnati.

Gwamnatin Assad dai ta yi alkawalin yin afuwa ga ‘yan tawayen idan sun amince su ajiye makamansu, tare da kiran taron hadin kan kasa domin kawo karshen rikicin da ya lakume rayukan mutane sama da 310,000 da raba rabin ‘Yan kasar da gidajensu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.