Isa ga babban shafi
Amurka

Obama ya gargadi Trump

Shugaban Amurka mai barin gado Barack Obama ya ce bayan ya sauka ba zai yi shiru ba idan har Donald Trump ya nemi dagula lamurran Amurka.

Barack Hussian Obama Shugaban Amurka na 44
Barack Hussian Obama Shugaban Amurka na 44 REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Obama wanda ya yi ganawar karshe da manema labarai a jiya Laraba ya tabbatarwa Amurkawa cewa ba za a samu matsala ba.

Sannan Obama ya roki Trump da kada ya gwama batun takunkumi da aka malkayawa Rasha da batun nukiliya.

A gobe Juma’a ne za a rantsar da Donald Trump a matsayin shugaban Amurka bayan da ya lashe zaben kasar da aka gudanar a ranar 8 ga watan Nuwamba.

Trump mai jiran gado ya fadi cikin wata tattaunawa da shi cewa zai ba Rasha tayin dage takunkumi idan har za ta rage ayyukanta na mallakan makaman nukiliya.

Obama wanda ya yi shekaru takwas yana mulki a Amurka ya ce ba zai rika gani ya yi shiru ba, bayan ya mika mulki a gobe Juma’a.

A lokacin yakin neman zaben shi, Donald Trump ya sha alwashin haramtawa musulmi shiga Amurka tare da korar bakin da ba su da takardu, yawancinsu ‘Yan Latin Amurka.

Obama ya ce ya ba Trump dukkanin shawarwarin da suka wajaba a ganawar da suka yi, domin shugabancin Amurka aiki ne da dole sai mutum nemi taimako.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.