Isa ga babban shafi
Amurka

Wata mace ta shigar da karar Trump a kotu

Wata mace ta shigar da karar shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump a kotun birnin New York bayan ta zarge shi da yunkurin lalata da ita da karfin tsiya.

Summer Zervos da ta shigar da karar Donald Trump a kotu
Summer Zervos da ta shigar da karar Donald Trump a kotu REUTERS/Kevork Djansezian
Talla

Summer Zervos da ta zargi Trump da kwakume ta a shekarar 2007 a wani daki na Otel din Beverly Hills, ta ce ya yi wa Amurukawa karya game da halayensa.

Sannan ta bayyana Trump da zai sha rantsuwar kama aiki a ranar Jumma’a mai zuwa a matsayin mai cin mutuncin mata wanda kuma ya ci zarafinta.

Zervos ta shaida wa ‘yan jarida a birnin Los Angeles cewa, ta dauki matakin maka Trump a kotu ne bayan ya ki bada hakuri kamar yadda ta bukata.

Zervos na daya daga cikin mata da dama da suka fito fili suna bayyana irin cin zarafin da Trump ya yi musu.

Sai dai Mr. Trump ya musanta dukkanin zarge-zargen tare da daukan alwashin shigar da karar su a kotu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.