Isa ga babban shafi
Amurka

Ba ni da wata alaka da Rasha- Trump

Shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump ya karyata zargin Rasha ta taimaka ma sa da bayanan sirri a kutsen da ta yi wa kasar a lokacin yakin neman zaben shi. Rasha ma ta karyata zargin, wanda ta kira kokarin kara dagula dangantar da ke tsakaninta da Amurka.

Shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump.
Shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump. REUTERS/Mike Segar/File Photo
Talla

Trump ya musanta zargin ne a shafin shi na Twitter inda ya ce Rasha ba ta taba yin amfani da shi ba, kuma baya da alaka ita.

Ya ce bai kamata hukumomin leken asirin Amurka su bari a yada zancen da ya kira na karya ga jama’a ba.

Kakakin gwamnatin Rasha ma Dmitry Peskov ya fito ya musanta zargin sun taimakawa Trump da bayanan na sirri, inda ya ce ana kokarin ne a kara dagula dangantar Amurka da Rasha da suke kokarin farfadowa.

Kafar Buzzfeed da ke yada labarai a intanet a Amurka ce ta wallafa rahoton mai shafi 35 akan Trump da kuma alakar shi da Rasha.

Rahoton kuma ya ce Trump ya ta yin musayar bayanai a lokacin yakin neman zaben shi tsakanin shi da wakilan gwamnatin Rasha. Bayanan kuma sun shafi kutsen da Rasha ta yi wa jam’iyyar Democrat da imel din yar takarar jam’iyyar Hillary Clinton.

Babu dai kyakkyawar alaka tsakanin Rasha da Amurka a zamanin Obama, amma Trump na da ra’ayin gwamnatin Putin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.