Isa ga babban shafi
Amurka

Putin ya nemi taimakawa Trump a Zabe-Rahoto

Wani rahoto da hukumomin leken asirin Amurka suka fitar na cewa shugaban Rasha Vladimir Putin ya nemi ya bai wa Donald Trump taimakon lashe zaben da aka yi a watan Nuwamba a kasar.

Cece-kuce kan nasaran Donald Trump a zaben Amurka bai kare ba
Cece-kuce kan nasaran Donald Trump a zaben Amurka bai kare ba REUTERS/Jonathan Ernst
Talla

Hukumomin na Rasha ba su ce komai a game da wannan zargi ba, ko da dai a baya Rasha ta sha musanta zargin.

Sai dai Bayan hukumomin leken asirin Amurkan sun yi wa shugaban mai jiran gado Mista Trump bayani kan sakamakon binciken da suka gudanar, ya ce rawar da Rasha ta taka a zaben ba ta yi tasiri a kan sakamakonsa ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.