Isa ga babban shafi
Syria

Ana ci gaba da fada a Syria duk an tsagaita wuta

Kwana daya bayan da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da wani shirin tsagaita wuta a Syria, rahotanni sun ce ana ci gaba da fada a sassa da dama na kasar.

An shafe shekaru 6 shida ana yaki a Syria
An shafe shekaru 6 shida ana yaki a Syria KARAM AL-MASRI / AFP
Talla

Shirin zaman lafiyar da Rasha da Turkiya suka gabatar ya samu karbuwa a zauren Majalisar Dinkin Duniya, amma rahotanni tun a jiya lahadi ke cewa jiragen yakin gwamnati sun kai wasu sabbin hare-hare akan yankunan ‘yan tawaye.

Jiragen Yakin gwamnatin na kai hare haren ne a garin Atareb da ke ikon ‘Yan tawaye a arewacin Syria

A ranar Alhamis ne yarjejeniyar tsagaita wutar tsakanin gwamnati da ‘Yan tawaye ta fara aiki amma rahotanni sun ce an kashe fararen hula hudu da suka hada da yara kanana guda biyu sannan an kashe ‘Yan tawaye guda Tara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.