'Yan Jaridu 93 ne suka rasa rayukansu a shekara ta 2016-IFJ
Yayinda muka yi bankwana da shekarar 2016, kungiyar ‘yan Jaridu ta duniya IFJ ta bayyana cewa, akalla ‘yan jaridun 93 aka kashe a cikin shekarar ta 2016.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Kungiyar ta IFJ ta ce kasashen Afghanistan da Iraqi ke kan gaba, wajen zama mafi hadari ga ‘yan Jaridu a cikin shekarar.
Rahoton yayi Karin bayanin cewa, yan jaridu 30 ne suka rasa rayukansu a gabas ta tsakiya kadai, inda ya zama mafi hadari garesu, yayinda aka kashe ‘yan jaridu 28 a nahiyar Asiya da yankin Pacific, a nahiyar Africa kuma guda 8 suka rasa rayukansu, yayinda a nahiyar turai ‘yan jaridu 3 suka salwanta.
Sai dai kuma a cewar kungiyar kare ‘yan jaridun ta Duniya, doka ta bi hakkin kashi 4 cikin 100 ne kawai daga cikin yawan ‘yan jaridun da aka kashe.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu