Isa ga babban shafi
Lake Chad

Rikicin Boko Haram ya yi muni a shekarar 2016

Wani bincike ya nuna cewar rikicin Boko Haram a yankin tafkin Chadi wanda ya mayar da mutane sama da miliyan 8 matalauta kuma ke barazanar haifar da yunwa, shi ne mafi girma a daukacin shekarar 2016.

Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau.
Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau. HO / BOKO HARAM AFP / AFP
Talla

Binciken da kamfanin dillancin labaran Reuters ya gudanar ya nuna cewar, bayan rikicin Boko Haram, tashin hankalin da ake yi a kasar Yemen shi ne mafi muni, ganin yadda kananan yara ke mutuwa da yunwa, sai kuma Sudan ta Kudu wadda Majalisar Dinkin Duniya ta ce, tana gaf da fadawa cikin kisan kare dangi.

Rahotan binciken ya ce, rikicin Syria da Iraqi sun dauke hankalin kasahsen duniya, amma halin da mutanen da rikicin Boko Haram ya ritsa da su na tashin hankali baya misaltuwa, kamar yadda kungiyoyin agaji  da ke yankin ke cewa.

Suzanna Tkalec, wata Daraktar kungiyar agaji ta Caritas ta ce, hankalinta na tashi da rikicin Syria, amma kuma halin tagayyara da mutanen da rikicin Boko Haram ya shafa a Najeriya da Nijar da kuma yadda kafofin yada labarai suka kauda kansu kan rashin abinci da kuma kayan agaji baya misaltuwa.

Ita ma kungiyar agaji ta Oxfam ta ce, akalla mutane miliyan 7 ba su da abincin da za su ci kuma kai musu dauki daga kungiyoyin agaji na da wahala saboda halin da yankin ke ciki.

Laura Lie ta kungiyar agajin CARE ta ce, yara 8 ne cikin ko wadanne 10 ke fama da tsananin yunwa a Yemen, kuma guda na mutuwa a duk mintina 10.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.