Isa ga babban shafi
EU-Kenya

EU ta musanta shisshigi a zaben Kenya

Ofisoshin jakadancin kasashen Turai 11 da kuma kungiyar tarayyar Turai, sun musanta zargin da hukumomin Kenya ke yi wa kasashen na yin shisshigi dangane da shirye-shiryen zaben kasar da za a yi a shekara mai zuwa.

Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta
Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta TONY KARUMBA / AFP
Talla

Jakadojin kasashen da suka fitar da wannan sanarwa dai sun hada da na Amurka, Canada, Jamus, Sweden, Australia da kuma Birtaniya, sauran kuwa su ne Holland, Danemark, Finland, Norway da kuma kungiyar tarayyar Turai.

Sanarwar dai ta fito ne kwana daya bayan da hukumomi a kasar ta Kenya sun dakatar da ayyukan wata kungiya mai zaman kanta da ke Amurka, wadda ke taimakawa dangane da yadda ake shirin gudanar da zaben na badi.

Duk da cewa Kenya ba ta fito fili karara ta bayyana abin da ta ke zargin kungiyar da aikatawa ba, amma gwamnatin ta ce, an dakatar da kungiyar ne da ke kan aiwatar da wani shirin inganta tsarin zabe da zai ci Euro milyan 19 saboda kungiyar ba ta da rajistar da ke ba ta damar daukar ‘yan asalin kasashen waje a matsayin ma’aikatanta.

Hukumomin na Kenya suka ce jami’an kungiyar na bukatar samun Bisar da ke ba su izinin yin aiki a kasar, kuma mako daya kafin nan, shugaba Uhuru Kenyatta da kansa ya zargi kasashen yamma da kokarin yin shisshigi game da zaben kasar mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.