Isa ga babban shafi
Cuba

A yau lahadi za a binne tokar gawar Fidel Castro a Santiago kasar Cuba

A safiyar yau lahadi ne, za a yi binne tokar gawar tsohon shugaban kasar Cuba Fidel Castro a makabartar  Santiagon kasar ta Cuba, a kusa da kabarin gwarzon neman yancin kan kasar, José Marti.  Bayan da ajiya assabar ayarin yan rakiyar gawar suka isa da ita a birnin Santiago  bayan tafiyar kwanaki uku da ta basu damar zagayawa da tokar gawar  a tafiya mai nisan kilo mita dubu 1000, daga Havane zuwa Santiago, inda za'a yi masa zanaizar  

shugaba Raúl Castro na Cuba na jagorantar shagulgulan jana izar dan uwansa Fidel Castro
shugaba Raúl Castro na Cuba na jagorantar shagulgulan jana izar dan uwansa Fidel Castro © Reuters
Talla

Marigayi Fidel Castro ya kaddamar da tawayensa ne a kusa da garin na Santiago, a shekarar 1950, ya kuma mutu a ranar 25 ga watan Nobemba da ya gabata bayan share tsawon shekaru 90 raye a duniya.

Kawo yanzu dai Mahukumta ba su bayyana dalilin mutuwarsa ba, sai dai an san cewa, koshin lafiyarsa na da rauni sosai, tun lokacin da ya kamu da wata matsananciyar rashin lafiyar da ta so kashe shi a 2006.

Wace kuma a kanta ne ya sallada jan ragamar kasar ga karamin kanensa Raul Castro, da a yau shima ke da shekaru 85 a duniya
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.