Isa ga babban shafi
China-Amurka

China ta yi wa Amurka korafi kan Trump

Gwamnatin China ta yi wa Amurka korafi bayan zababben shugabanta mai jiran gado Donald Trump ya zanta da shugabar Yankin Taiwan, Tsai Ing-Wen ta wayar tarho. 

Shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump
Shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump REUTERS/Jonathan Ernst/File Photo
Talla

Kasar China dai na kallon Taiwan a matsayin yankinta da ya balle, yayin da Amurka ta yanke huldar diflomasniya da yankin shekaru 37 da suka gabata tare da bayyana Beijing a matayin gwamnatin da ta amince da ita.

A karon farko kenan cikin wadannan shekarun da wani shugaban Amurka ya zanta kai tsaye ta wayar tarho da shugaban yankin na Taiwan.

Rohatanni sun ce, shugabannin biyu sun tattauna kan huldar kasuwanci da siyasa da kuma samar da tsaro.

Kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya rawaito cewa, gwamnatin China ta bukaci Amurka da ta yi taka-tsan-tsan kan batun Taiwan, don kauce wa sukurkucewar alakar da ke tsakaninsu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.