Isa ga babban shafi
Syria

Aleppo na son komawa makabarta

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewar birnin Aleppo ya zama kamar wata babbar makabartar da za a samu a duniya muddin kwamitin Sulhu ya kasa kawo karshen halin da ake ciki da kuma tabbatar da kai kayan agaji ga mutanen da ke birnin.

Dakarun Syria na ci gaba da yakar 'Yan tawaye a yankin Aleppo
Dakarun Syria na ci gaba da yakar 'Yan tawaye a yankin Aleppo REUTERS
Talla

Babban jami’in Jinkai na Majalisar Stephaine O’Brien ya yi kira ga wakilan kwamitin Sulhun da su yi wa Allah su janyo hankalin bangarorin da ke rikici su kare fararen hular da tashin hankalin ya tagayyara yanzu haka.

Jami’in ya ce yanzu haka mutane suna cikin yunwa tare da neman abinda za su ci, yayin da babu magunguna a asibitoci sakamakon hare haren da sojojin Syria ke kai wa, abinda ya tilastawa mutane sama da 25,000 tserewa.

Birtaniya ta zargi Rasha da hana daukar mataki, yayin da Rasha ke cewa Syria na kai harin ne kan yan ta’adda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.