Isa ga babban shafi
Duniya

Ayyukan Mutane biliyan 1.4 na dogaro ne da furanni

Wani sakamakon binciken masana ya ce kusan ayyukan mutane biliyan daya da rabi da yawancin amfanin gona na dogaro ne da nau’in wasu kwari da ke cin furanni, wanda kuma ke barazana ga jin dadin jama’a idan har ba a kawo karshen farautar irinsu kudan zuma ba da malam bude littafi.

Furanni ne abincin Malam Bude Littafi
Furanni ne abincin Malam Bude Littafi Getty Images/Sarah Orsag
Talla

Binciken na masana a Jami’ar Reading tare da hadin guiwar wasu masana a sassan duniya ya ce wadatar abinci da ayyuka na fuskantar barazana idan har ba a gaggauta daukar matakan kawo karshen karancin na’ukan kwarin ba da ke samar da abinci ko wasu bukatun al’umma.

Kwarin sun hada da Kudan zuma da malam bude littafi da tsuntsaye, kamar jemagu da kadangaru yayin da wasu ke samar da amfanin daga iska.

Furanni ne abincin Kudan Zuma
Furanni ne abincin Kudan Zuma wonderopolis

Sannan abin da suke bayarwa ya shafi kai tsaye kashi uku cikin hudu na mafi muhimmacin amfanin gona da suka hada ‘yayan itace da iri da kuma masu daraja kamar cocoa da zaitun.

Binciken ya ce ana iya samun karuwar cututtuka da za a iya magancewa saboda karewar yawan kwarin ko tsuntsayen da ke cin furanni.

Mutane biliyan daya da dubu dari hudu ke aiki a bangaren noma a cewar binciken, wato kashi guda cikin uku na adadin yawan ma’aikatan kwadago a duniya.

Jemagu na cin Furanni
Jemagu na cin Furanni http://blog.nwf.org

Kuma yawancin manoma da kuma masu ci karkashin aikin noma sun fi yawa a karkara a kananan kasashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.