Tsohon Shugaban Fidel Castro na Cuba ya rasu
Kasar Cuba ta ayyana zaman makokin kwanaki 9 sakamakon mutuwar tsohon shugabanta Fidel Castro wanda ya mutu yana mai shekaru 90.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Mutuwar da kanin Marigayin, Shugaba Raul Castro, ya sanar ya ce Shugaban juyin-juya-halin Kwaminisancin ya mutu ne da a daren jiya, kuma za a kona gawarsa karshan mako mai kamawa.
Fidel Castro wanda ake zargi da murkushe 'yan adawa, ya shugabanci Cuba a matsayin kasa mai bin jam'iyya guda na tsawon kusan shekara 50 kafin dan uwansa Raul ya karbi mulki a shekarar 2006.
Tuni shugabanni duniya suka fara aike sako da jimamin mutuwar tsohon shugaban na Cuba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu