Isa ga babban shafi
Cuba

Shugabanin Duniya na alhinin mutuwar Fidel Castro

Shugabanin Kasashen Duniya na ci gaba da bayyana alhinin su na rasuwar tsohon shugaban kasar Cuba, Fidel Castro.

Tsohon Shugaban kasar Cuba Fidel Castro
Tsohon Shugaban kasar Cuba Fidel Castro REUTERS/Claudia Daut
Talla

Shugaba Barack Obama yace tarihi zai nunawa duniya irin rawar da marigayin ya taka wajen gina Cuba, yayin da a karkashin shugabancin sa ya mayar da huldar dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya bayyana Castro a matsayin mutumin da sunan sa ba zai bata ba a tarihin duniya.

Tsohon shugaban Tayyara Soviet, Mikhail Gorbachev, ya bayyana Castro a matsayin mutumin da ya kare martabar kasar sa duk da tsananin matsin lambar da ya samu daga Amurka.
Shugaban kasar China Xi Jingpin yace mutanen China sun rasa aboki mutumin kirki.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana Castro a matsayin abokin Afirka wanda ya bada gudumawa wajen bunkasa ilimi da lafiyar mutanen ta.

Shugaba Francois Hollande na Faransa ya bayyana marigayin a matsayin mutumin da ya jagoranci juyin juya halin da ya ‘yantar da Cuba.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon ya mika ta’aziyar sa ga mutanen Cuba saboda rasa gwarzon su, inda ya bayyana goyan bayan Majalisar ga mutanen Cuba.

Firaministan India Narendra Modi ya bayyana Castro a matsayin daya daga cikin fitattun mutanen karni na 20.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.