Isa ga babban shafi
Bincike

Kare na da dogon tunani

Wani Binciken masana da aka gudanar a wata babbar cibiyar bincike a Budapest kasar Hungary ya nuna cewar karnuka na da tunanin da ya zarce yadda aka sani, wajen tuna huldarsu da mutane da abin da mutane suka musu.

Kare na da kaifin basira
Kare na da kaifin basira REUTERS
Talla

Binciken ya nuna cewar karnukan na iya tuna abin da ya faru na dogon lokaci kamar yadda Dan Adam ke yi, duk da ya ke ba wai bayani suke yi da za a gane ba.

Shugaban masanan da suka gudanar da binciken Claudia Fugazza ta yi misali da yadda ake koyawa karnukan wasu halaye, kuma idan aka dauki dogon lokaci aka umurce su, sukan iya yin abin da aka koya musu.

Binciken na masanan halittu ya ce Karnuka na da dogon tunanin da ba su mantuwa.

Jami’ar tace wannan ya sa sau da yawa idan ka yi wa kare laifi, duk tsawon lokacin da ka dauka ba ku hadu ba, da zaran ya gan ka zai tuna.

Wannan dai shi ne bincike na farko da aka gudanar akan kaifin basirar wata halitta kamar ta dan adam.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.