Isa ga babban shafi
Morocco

An kammala taron dumamar yanayi a Morocco

Yau ne ranar karshe da ake rufe babban taron Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi  a birnin Marrakesh na Morocco, in da ake sa ran amincewa da yarjejeniyar Paris duk da barazanar da zababben shugaban Amurka Donald Trump ya yi na yin watsi da yarjejeniyar.

Kasashen duniya na kammala taron dumamar yanayi a birnin Marrakesh na Morocco
Kasashen duniya na kammala taron dumamar yanayi a birnin Marrakesh na Morocco RFI
Talla

Babban kalubalen da ke gaban wakilan kasashe 196 a taron sauyin yanayin, shi ne yadda za su aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla a birnin Paris na Faransa kan rage fitar da hayaki mai gurbata muhalli a duniya.

Sai dai kuma ikirarin Donald Trump na yin watsi da yarjejeniyar na a matsayin cikas ga muradin da ake son cimma na aiwatar da yarjejeniyar, musamman biliyoyan kudin tallafi da aka yi alkawalin bai wa kananan kasashe da suka fi shan wahalar matsalolin dumamar yanayi.

Yarjejeniyar Paris dai da ake son aiwatarwa ta kunshi rage dumama yanayi da kashi biyu na ma’aunin celsius, tare da da rage gurbataccen iskar da masana’untun manyan kasashe ke fitarwa.

Amurka dai na cikin kasashen duniya da suka sa hannu a yarjejeniyar kuma masana na ganin yana da wahala a cimma biyan bukata ba tare da Amurka ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.