Isa ga babban shafi
Bankin Duniya

Bala’o’i na jefa mutane miliyan 26 cikin talauci a shekara

Wani rahoton Bankin Duniya ya ce annobar balo’oi kamar ambaliyar ruwa da fari na jefa mutane akalla miliyan 26 cikin talauci duk shekara tare da hasarar kudi sama da dala biliyan 500 baya ga dimbin dukiyar da ake yin hasara.

Matsalolin ambaliya da fari da canjin yanayi ke haifarwa na jefa miliyoyan mutane cikin talauci
Matsalolin ambaliya da fari da canjin yanayi ke haifarwa na jefa miliyoyan mutane cikin talauci REUTERS/Cheryl Ravelo
Talla

Bankin Duniya ya wallafa rahoton ne a zauren taron tattauna matsalar canjin yanayi a Morocco.

Rahoton ya yi gargadin cewa adadin zai ci gaba da karuwa idan har ba a dauki matakan magance matsalar dumamar yanayi ba da ke haifar da bala’o’in da ke jefa mutane cikin wahala.

Rahoton mai shafi 190 ya bayyana damuwa akan yadda ba a damu da girman barnar da matsalar yanayi ke haifarwa ba domin yin gaggawar gina talakawan da bala’oin ke shafa.

Rahoton ya ce akwai bukatar a san inda ya dace da yadda za a dauki matakai a birane da karkara domin kare jama’a daga matsalolin da yanayin ke kawo wa.

A cewar rahoton mafi yawancin gwamnatoci sun fi mayar da hankali a unguwannin attajirai wajen daukar matakan kare ambaliyar ruwa.

Binciken rahoton a kasashe 117 da suka kunshi masu arziki da masu tasowa ya tabbatar da hasarar kudi sama da dala biliyan 327 .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.