Isa ga babban shafi
morocco

Kasashen duniya na taron dumamar yanayi a Morocco

Jakadun kasashen duniya 196 sun fara gudanar da tattaunawa a birnin Marrakesh na kasar Morocco da zimmar aiwatar da yarjejeniyar magance matsalar dimamar yanayi da aka cimma a cikin watan Disamban bara a birnin Paris na Faransa.

Jakadun kasashen duniya 196 ne ke halartar taron sauyin yanayi a birnin Marrakesh na Morocco
Jakadun kasashen duniya 196 ne ke halartar taron sauyin yanayi a birnin Marrakesh na Morocco REUTERS/Stephane de Sakutin
Talla

An bude taron na yau ne a dai dai lokacin da yarjejeniyar ta Paris ke fuskantar barazana daga bangaren dan takaran shugabancin Amurka karkashin jam’iyyar Republican Donald Trump.

Bayan ta gudanar da jawabin bude taron, Ministar muhalli ta Faransa, Segolene Royal ta mika ragamar gudanar da taron a hannun ministan harkokin wajen Morocco Salaheddine Mezouar.

A jawabinta, Royal ta bayyana cewa, kasashen duniya 100 sun rattaba hannu kan yarjejeniyar ta Paris wadda ta fara aiki gadan-gadan a ranar jumma’ar da ta wuce.

Wannan dai na zuwa ne a yayin da ake ci gaba da dari-dari kan matsalar sauyin yanayin da kuma illolinta.

To sai a yayin da ake gudanar da wannan taron na kwanaki 12 da ke samun halartar mutane kimanin dubu 15, hankulan jama’ar duniya sun karkata ne kan babban zaben Amurka da za gudanar a gobe Talata, in da ake ganin watakila Donald Trump ya samu nasara.

Duk da dai ana ganin Trump ba zai iya warware yarjejeniyar ba, amma masana sun ce, nasararsa a zaben za ta iya haifar da nakasu ga yarjejeniyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.