Isa ga babban shafi
Amurka

Clinton ba ta aikata laifi ba- FBI

Shugaban hukumar bincike ta Amurka James Comey ya ce, basu gano wani laifi da Hillary Clinton da ke takarar shugabancin kasar ta aikata ba a binciken sakwanninta na Imel da suke yi.

Hillary Clinton ta jam'iyyar Democrat a Amurka
Hillary Clinton ta jam'iyyar Democrat a Amurka REUTERS/Brian Snyder
Talla

Yayin jawabi ga 'yan majalisun kasar, Comey ya ce binciken nasu bai sa sun gano abin da zai sauya matsayinsu na baya cewar, babu wani laifin da zai sa a iya gurfanar da ita a gaban shari’a ba.

Wannan matsayi ya kwantar da hankalin 'ya'yan Jam’iyyar Democrat, sai dai suna zargin cewar kalaman shugaban na FBI ya yi wa takarar Clinton illa.

Sai dai Newt Gingrich, mai bai wa Donald Trump shawara ya bayyana cewar, shugaban na FBI ya fuskanci matsin lamba ne don ganin ya wanke 'yar takarar

A bangare guda, yau ake kammala yakin neman zaben shugabancin kasar, in da 'yan takaran biyu ke ci gaba da karade wuraren da suke ganin ya dace su samu karin goyan bayan jama'a don samun nasara.

Rahotanni sun ce, shugaba Barack Obama da Uwargidansa Michelle Obama da Bill Clinton za su halarci gangami na karshe don janyo hankalin Amurkawa, yayin da  Trump ke ci gaba da sukar Hillary, in da ya bayyana zabenta a matsayin hadari ga al'ummar kasar.

Bayanai sun ce, mutanen Latino da Trump ke barazanar korar su daga kasar na ta tururuwa suna cika rumfunan zabe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.