Isa ga babban shafi
EU-Canada

EU ta cimma yarjejeniyar kasuwanci da Canada

Kungiyar tarayyar Turai ta cimma yarjejeniyar kasuwanci da aka yi wa lakabi da CETA da Canada, bayan tsaikon da aka samu saboda wani yanki na Belgium da ya nuna adawa da shirin kulla yarjejeniyar.

Firaministan Canada  Justin Trudeau da shugaban hukumar tarayyar Turai  Jean-Claude Juncker bayan cimma yarjejeniyar CETA a ranar 30 ga watan Oktoba na shekarar 2016
Firaministan Canada Justin Trudeau da shugaban hukumar tarayyar Turai Jean-Claude Juncker bayan cimma yarjejeniyar CETA a ranar 30 ga watan Oktoba na shekarar 2016 REUTERS/Eric Vidal
Talla

Firaministan Canada, Justin Trudeau ne ya rattaba hannu kan yarjejniyar cinikayyar da manyan jami’an kungiyar tarayyar Turai bayan yankin Wallonia na Belgium mai jumullar mutane miliyan 3.6 ya amince da shirin.

Tun ranar Alhamis da ta gabata ne, bangarorin biyu suka shirya cimma matsaya kan wannan batu, amma hakan ya ci tura saboda yankin Wallonia da ya yi watsi da yarjejeniyar da ake sa ran mutane fiye da miliyan 500 za su ci gaciyarta.

A ranar Jumma’a ne ilahirin mambobin kasashen tarayyar Turai 28 suka cimma matsaya a tsakaninsu kamar yadda sharadin yarjejeniyar ya bukata.

Masu ruwa da tsaki a cikin lamarin na ganin cewa, yarjejeniya za ta kara bunkasa harkar kasuwanci da kudin da yawansa ya kai Dala biliyan 12 a duk shekara, sannan kuma za ta shafe kashi 99 cikin 100 na kudaden haraji da jami’an hana fasa kuari ke karba, baya ga ayyukan yi  masu gwabi da yarjejeniyar za ta kawo tsakanin matasan Turai da Canada.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.