Isa ga babban shafi
Faransa-Syria

Faransa ta fara binciken gwamnatin Syria

A karon farko bangaren shari’a na kasar Faransa ya sanar da fara bincike a game da laifufukan da ake zargin gwmanatin Bashar Assad da aikatawa a Syria, inda tuni aka fara tuhumar wasu mutane da ake zargi da hannu wajen aikata laifufuka a rikicin kasar.

Shugaban kasar Syria Bashar al-Assad
Shugaban kasar Syria Bashar al-Assad REUTERS
Talla

Wasu daga cikin zarge-zargen da kotun ta fara bincike a kai sun hada da wasu ‘yan Syria biyu da ke da takardar shaidar zama Faransawa da suka bata a Syria tun shekara ta 2013.

Bayanai na nuni da cewa mutanen biyu hukumomin Syria ne suka kama su, kuma tun daga wannan lokaci har yanzu ba a ji duriyarsu ba, wannan ne ya sa ma’aikatar shari’a ta kasar ta nada alkalai uku domin binciken zarge-zargen.

Kafin dai Faransa ta dauki wannan mataki, akwai wasu kasashe na Turai da dama da suka fara binciken a cikin gida kan laifufukan da aka aikata a Syria, da suka hada da Jamus da Holland da kuma Birtaniya.

Faransa za ta fadada binciken zuwa sauran laifufuka da aka aikata a Syria, a daidai lokacin da ake zargin gwamnati da kuma sauran kungiyoyin da ke dauke da makamai da aikata laifufuka daban daban a wannan yaki da ya share kusan shekaru shida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.