Saurare Saukewa Podcast
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 19/10 06h00 GMT
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 21/10 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 21/10 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 19/10 06h17 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 19/10 07h00 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 20/10 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 20/10 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 19/10 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 20/10 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 19/10 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 20/10 16h06 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 20/10 16h30 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 19/10 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 20/10 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 19/10 16h40 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 19/10 20h00 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 20/10 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 20/10 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 19/10 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Gaggauce

Sanata Shehu Sani mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya a arewacin Najeriya ya sanar da ficewa daga Jam'iyyar APC mai mulkin kasar.
Sani wanda ya mika takaddar ficewa daga Jam'iyyar ga shugabanta na kasa Adams Oshimole bai sanar da dalilin ficewarsa ba, haka zalika bai fadi Jam'iyyar da zai koma ba.

Duniya

Ana zanga-zangar kin jin Maduro a Venezuela

media Zanga-zangar adawa da shugaban Venezuela Nicolas Maduro. REUTERS/Carlos Eduardo Ramirez

‘Yan adawar Venezuela na ci gaba matsin lamba kan shugaba Nicolas Maduro ya sauka daga kujerarsa yayin da suka sanar da shirin gudanar da sabuwar zanga-zanga da yajin aikin gama-gari.

‘Yan adawar sun bukaci gudanar da yajin aikin gama–gari har na tsawon sa’oi 12 a gobe juma’a kuma sun lashi takobin amfani da yawansu a majalisar dokokin kasar don fitar da sanarwa kan yadda shugaba Maduro ya tafiyar da tattalin arzikin kasar da ya tabarbare.

Shugaban majalisar tarayyar kasar Henry Ramos Allup ya bayyana cewa, za su sanar da Maduro cewa, al’ummar Venezuela sun dauke shi a matsayin shugaban da ya gaza gudanar da ayyukansa.

Mista Allup da ke Magana a gaban masu zanga-zanga a Caracas babban birnin kasar ya ce za su amince a gudanar da gangami a fadar shugaban kasa a ranar 3 ga watan Nuwamba.

Kimanin mutane miliyan 1 da dubu 200 ne suka yi gangami a babban birnin kasar kamar yadda ‘yan adawar suka sanar, kuma wannan shi ne adadin mutane mafi girma da suka shiga zanga-zangar kwana guda a duk fadin kasar.

Sai dai an samu tarzoma a wasu sasan kasar a lokacin gudanar da zanga-zangar abinda ya yi sanadiyar mutuwar dan sanda guda a jihar Miranda.

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure