Isa ga babban shafi
Venezuela

An yi zanga-zangar adawa da Moduro na Venezuela

'Yan adawar kasar Venezuela sun gudanar da zanga-zanga a titunan Caracas don ci gaba da matsin lambar da suke yi wa shugaba Nicolas Maduro na ganin ya sauka daga kujerarsa.

Shugaba Nicolás Maduro na Venezuela
Shugaba Nicolás Maduro na Venezuela Fuente: Reuters.
Talla

A makon jiya, majalisar kasar ta yi kira ga al’umma don fitowa su yi zanga zangar saboda yadda kotun koli ta hana yunkurin gudanar da zaben raba gardama.

'Yan majalisun sun kuma amince da shirin gayyato shugaba Maduro majalisar don amsa tambayoyi, abin da shugaban ya yi watsi da shi.

A karshen mako fadar Vatican ta ce, shugaban da wani bangare na 'yan adawar kasar sun amince su fara tattaunawa a tsakaninsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.