Isa ga babban shafi
NATO

NATO ta dauki mataki kan Rasha

Kungiyar tsaro ta NATO na shirin matsin lamba kan mambobinta don bayar da gudun mawa wajen karfafa aikin sojinta a kan iyakokin kasar Rasha. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da NATO ke shirin tsawaita yakin cacar baka da gwamnatin Moscow wadda ta mamaye yakin Crimea na Ukraine. 

Sakatare Janar na NATO Jens Stoltenberg
Sakatare Janar na NATO Jens Stoltenberg REUTERS/David Mdzinarishvili
Talla

A yayin da jirgin Rasha ke ratsawa ta yankin kasashen Turai da nufin shiga kasar Syria mai fama da rikici, ministocin tsaro na kasashen NATO na kokarin cika alkawarin da shugabanninsu suka dauka a cikin watan Juli na aike wa da dakaru zuwa yankin kasashen Baltics da kuma gabashin kasar Poland nan da farkon shekarar badi.

Wannan dai wani mataki ne na ganin cewa, Rasha ba ta mamaye kan iyakokin kasashen Baltics da Poland ba kamar yadda ta yi nasarar mamaye Crimea na Ukraine, abin da ya haifar mata da tsamin danganta da kasashen yamma.

Dangantakar Rasha da kasashen na yamma ta kara tsami bayan da ta gaza cimma matsaya da Amurka don kawo karshen rikicin Syria.

Sannan kuma Amurka ta sake zargin Rasha da yunkurin haifar mata da cikas a zaben shugabancin kasa da za ta gudanar nan da watan gobe ta hanyar kutse a shafin intanet.

Har ila yau, a makon jiya ne, kasashen Turai suka gana kan batun sanya sabbin takunkumai kan Rasha saboda rawar da ta ke takawa a yakin Syria musamman a birnin Aleppo, in da ta ke kai hare-hare kan fararen hula.

A bangare guda, kasar Rasha ta janye bukatar ganin jiran ruwanta na yakin su sha mai a Spain kafin su isa Syria don ci gaba da kai hare-hare, kuma hakan na zuwa bayan matsin lamban da Spain ta sha daga NATO.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.