Isa ga babban shafi
Libya

MSF ta gano gawarwakin 'yan cirani a teku

Kungiyar likitoci ta Medicins Sans Frontieres ta ce jami’anta sun gano gawarwakin mutane 25 a cikin wani karamin kwale-kwale kusa da gabar ruwan kasar Libya.

Wasu daga cikn 'yan cirani da ke son tsallakawa Turai don samun ingantacciyar rayuwa
Wasu daga cikn 'yan cirani da ke son tsallakawa Turai don samun ingantacciyar rayuwa ARIS MESSINIS / AFP
Talla

Kungiyar ta MSF ta ce jirgin ruwa da ke sintiri akan teku domin tallafa wa bakin-haure da ke kokarin tsallaka tekun Meditarranean zuwa Turai, shi ne ya gano wadannan gawarwaki 25 tare da ceto wasu mutanen su 107 a tsakiyar teku.

Wani jami’i a kungiyar ta Medecins Sans Frontieres ya ce, 23 daga cikin gawarwakin na da alamun kunar wuta, yayin da 11 ke da wasu alamun da ke tabbatar da cewa sun sha wuya kafin mutuwarsu.
 

Kafin nan, wasu kungiyoyin masu zaman kansu sun sanar da ceto ‘yan ci rani 139 da suka tashi daga gabar ruwan na Libya dukkaninsu da niyyar zuwa Turai duk da irin hatsarin da ke tattare da wannan tafiya.
 

Daga farkon wannan shekara ta 2016 zuwa yanzu, alkaluma sun tabatar da mutuwar mutane dubu uku da 800 a daidai lokacin da suke kokarin tsallaka tekun na Meditarranean zuwa Turai, in da suke fatan samun ingantacciyar rayuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.