Isa ga babban shafi
Venezuela

Majalisar Venezuela ta gayyaci Maduro gaban ta

Majalisar Kasar Venezuela ta kada kuri’ar amincewa da bukatar gayyato shugaban kasar Nicolas Maduro dan gurfana a gaban ta dan amsa tambayoyi, bayan kotun kolin kasar ta ki amincewa da bukatar gudanar da zaben raba gardama.

Shugaban kasar Venezuela Nicolás Maduro na fuskantar matsin lamba zaben raba gardama a kasar
Shugaban kasar Venezuela Nicolás Maduro na fuskantar matsin lamba zaben raba gardama a kasar Fuente: Reuters.
Talla

Ana saran shugaba Maduro ya gurfana a gaban Majalisar ranar 1 ga watan gobe kan abinda 'yan majalisun suka kira karya dokar aiki.

Kotun kolin kasar ta bayyana yunkurin tsige shugaban a matsayin wanda ya saba ka’ida.

Tuni wani sashe na 'yan adawar kasar ya amince ya zauna teburin sasantawa da gwamnati sakamakon shiga tsakani da Paparoma Francis ya yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.