Isa ga babban shafi
Hakkin Mata

Ana samun ci gaba a cike gibin daidaito jinsi a duniya

Wani Bincike da Hukumar kula da tattalin arzikin duniya ta gudanar ya nuna mata cewar, an samu raguwa a shirin da akeyi na cike gibin da ake samu wajen daidaito tsakanin maza da mata wajen daukar ma’aikata a duniya.

Kafin a samu daidaiton da ake bukata tsakanin mata da maza a duniya, zai kai shekaru 170 masu zuwa
Kafin a samu daidaiton da ake bukata tsakanin mata da maza a duniya, zai kai shekaru 170 masu zuwa AFP PHOTO/Dibyangshu SARKAR
Talla

Rahotan binciken ya ce banda kasar Rwanda da aka samu ci gaba wajen baiwa mata damar tafiya kafada da kafada da maza a wuraren aiki, fagen siyasa da kuma daidaiton albashi, sauran kasashen duniya sun gaza.

Rahotan ya ce halin da ake ciki yau ya yi kama da yadda ake samun bambamci tsakanin mata da maza shekaru 53 da suka gabata.

A karshe binciken ya ce kafin a samu daidaiton da ake bukata tsakanin jinsinan biyu a duniya, zai kai shekarar 2186, wato shekaru 170 masu zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.