Isa ga babban shafi
Montenegro

DPS na sahun gaba a zaben Montenegro

Jam’iyyar DPS mai mulki a kasar Montenegro daya daga cikin tsoffin kasashen tarayyar Yougoslavia ce, ke sahun gaba ta fannin yawan kuri’u a zaben ‘yan majalisar da aka gudanar a jiya lahadi.

Firaministan Montenegro Milo Djukanovic, a yayin murnar nasarar da ta jam'iyyarsa ta samu a zaben 'yan majalisa
Firaministan Montenegro Milo Djukanovic, a yayin murnar nasarar da ta jam'iyyarsa ta samu a zaben 'yan majalisa REUTERS/Stevo Vasiljevic
Talla

Wannan dai na nufin cewa masu ra’ayin kasashen Yammacin duniya ne suka yi nasara a kan ma’abota Rasha.
 

Alkaluman farko na sakamakon wannan zabe na tabbatar da jam’iyyar ta firaminista mai-ci Milo Djuka-Novic a matsayin wadda ta lashe kujeru 36 daga cikin 81 da ake da su a zauren majalisar dokokin kasar.

Har ila yau akwai wasu jam’iyyu na tsirarun kabilu a kasar ta Montenegro da suka hada da Bosniyawa da Kuroshiyawa da kuma Albaniyawa, da mafi yawan su ke goyon bayan kulla alaka da kungiyar tsaro ta NATO, kuma suka taka gagaruwar rawa a zaben na jiya.
 

Tun shekara ta 2012 ne wadannan jam’iyyun suka fara gwagwarmayar ganin kasar ta matso kusa da kasashen na Yammacin duniya, yayin da wasu ke fatan ci gaba da rike Rasha a matsayin abokiyar tafiya.
 

A jiya lahadi jami’an tsaron kasar sun sanar da kama mutane fiye da 20, wadanda aka ce sun shigo kasar ne daga Serbia da nufin aikata ta’addanci da kuma sace firaministan kasar domin yin garkuwa da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.