Isa ga babban shafi
MDD

MDD: An tabbatar da Guterres a matsayin Sakatare Janar

Taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya ya jefa kuri’ar amincewa da Antonio Guterres a matsayin sabon Sakatare Janar domin maye gurbin Ban-Ki-Moon wanda ke daf da kawo karshen wa’adin aikinsa.

Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da Antônio Guterres na Portugal a matsayin sabon Sakatare Janar
Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da Antônio Guterres na Portugal a matsayin sabon Sakatare Janar REUTERS/Rafael Marchante
Talla

Illahirin kasashen 193 da ke cikin babban zauren Majalisar ne suka amince da Guterres wanda tsohon Firaministan kasar Portigal ne.

Guterres zai jagoranci Majalisar Dinkin Duniya a wa’adin shekaru biyar daga ranar 1 ga watan Janairu mai zuwa.

Guterres ya taba zama shugaban hukumar kula da ‘Yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ana sa ran zai fi taka muhimmiyar rawa ga diflomasiyar duniya fiye da Ban Ki-moon da zai gada.

Zabin Guterres dai na zuwa ne a yayin da duniya ke fama da rikicin Syria da ya haifar da kwararar ‘yan gudun hijira da barazanar kungiyar IS kuma rikice-rikice a kasashen Yemen da sudan ta Kudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.