Isa ga babban shafi
MDD

An bar Yara Mata a baya

A Yau ne 11 ga watan Oktoba Majalisar Dinkin Duniya ta ware a matsayin ranar yara mata ta duniya domin jaddada muhimmacinsu tare nazari akan kalubalan da suke fuskanta.

Niger da Chadi da Najeriya na cikin kasashe mafi muni ga Yara mata.
Niger da Chadi da Najeriya na cikin kasashe mafi muni ga Yara mata. REUTERS/Akintunde Akinleye
Talla

Majalisar Dinkin Duniya ta ce yawan Yara Mata Biliyan daya da Miliyan daya wani bangare ne da zai taka muhimmiyar rawa ga ci gaban al’umma. Sai dai yara Mata na fuskantar koma-baya a kullum a sassan duniya.

Taken bikin bana shi ne “Ci gaban Yara mata shi ne ci gaban muradi”, tare da nazari ga abubuwan da suka ya shafe su.

A rahoton da ta wallafa a yau, kungiyar kare yara kanana ta Save The Children ta ce an bar yara Mata a baya saboda matsaloli na rashin daidaito da karfafawa Mata.

Kungiyar ta ce Dan Adam ba zai samu nasara da cikkaken ci gaba ba idan aka hanawa wani bangare na rabin al’umma samun ‘yancinsu a matsayinsu  'Yan Adam.

Save The Children ta zayyana matsaloli uku da ta ce suke tauye ci gaban mata da suka hada da Aure da wuri da rashin samun abubuwan more rayuwa da karfin fada aji ga harakoki na yau da kullum.

Rahoton kungiyar ya ce cikin dakika bakwai ana aurar da Yarinya ‘yar kasa da shekaru 15, sannan duk shekara ana aurar da Yara mata miliyan 15 ‘yan kasa da shekaru 18.

Rahoton ya ce ana aurar da Yara mata daya daga cikin uku a kasashe masu tasowa. Kuma matsalar ta fi shafar talakawa fiye da ‘yayan attajirai.

Rahoton na Save The Children ya ce a Najeriya kashi 40 na yara matan da ake wa auren-wuri ‘yayan talakawa ne da ba su da gata sabanin kashi 3 cikin 100 na ‘ya’yan masu hali.

Najeriya da Nijar da Mali da Habasha da Afrika ta tsakiya ne aka fi yin auren-wuri a cewar rahoton. Sannan Nijar ce ta karshe a matsayin kasa mafi muni ga yara mata.

Rahoton kuma ya ce a Kasashen India da Afghanistan da Yemen da Somalia an fi tursasawa yara ‘Yan kasa da shekaru 10 su auri masu manyan shekaru.

Akwai dai wasu kasashen Afrika da suka haramta aurar da yara ‘yan kasa da shekaru 18.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.