Isa ga babban shafi
Haiti

Guguwar Matthew ta kashe daruruwan mutane a Haiti

Jami’an ceto a kasar Haiti sun ce yawan mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon guguwar Matthew sun karu zuwa sama da 400. Yanzu haka kuma guguwar ta shiga Jihar Florida da ke Amurka cikin gudun kilomita kusan 200 a sa'a guda.

Guguwar na ci gaba da rusa gidaje da kada itatuwa da turakan lantarki
Guguwar na ci gaba da rusa gidaje da kada itatuwa da turakan lantarki REUTERS/Andres Martinez Casares
Talla

Gwamnatin Amurka ta kafa dokar ta-baci a Jihohin Georgia da Florida.

Rahotanni sun ce guguwar ta kashe mutane 50 a kudancin Roche-a-Bateau, bayan ta rusa gidaje da itatuwa da turakan lantarki.

Hukumomi sun ce akasarin inda aka samu mutuwar sun fito ne daga mutanen da ke zama a kauyuka da biranen da ke bakin teku, wadanda itatuwa ko turaku suka fadi a kan su.

Ofishin Jin-kai na Majalisar Dinkin Duniya ya ce mutane 350,000 yanzu haka ke bukatar agaji a kasar.

Yanzu haka Amurka ta bukaci mutane sama da miliyan 3 su kauracewa gidajensu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.