Isa ga babban shafi
Afghanistan

Kasashen duniya sun tallafa wa Afghanistan

Manyan kasashen duniya da ke ganawa a birnin Brussels sun yi alkawarin bai wa Afghanistan da yaki ya daidaita tallafin biliyoyin Dala nan da shekarar 2020.

Taron kasashen Turai da Afghanistan a birnin Brussels
Taron kasashen Turai da Afghanistan a birnin Brussels JOHN THYS / AFP
Talla

A wannan Laraba ne shugaban kasar Afghanistan Ashraf Ghani ya gana da hukumomin manyan kasashen duniya fiye da 70 da suka hada da sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry da kuma babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon a wani taro da ke gudana a birnin Brussels.

Shugabar harkokin wajen kasashen Turai, Federica Mogherini ta sanar cewa, tarayyar Turai mai mambobi 28 za ta bayar da gudunmawar Dala biliyan 1.5 a cikin shekara guda, yayin da ta yi fatan ganin sauran abokan huldarsu sun bi sahunsu.

Mogherini ta kara da cewa, manyan kasashen yankin Asiya da suka hada da China da India da Pakistan, sun cimma matsaya a cikin daren ranar Talata game da samar da hanyar tattaunawar zaman lafiyar Afghanistan.
Ita kuma kungiyar tarayyar Turai, za ta saukake hanyar zaman tattaunawar nan da wasu ‘yan watanni masu zuwa kamar yadda Mogherini ta bayyana.

A bangare guda, sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry ya bukaci kungiyar Taliban da ta bi sahun Gulbuddin Hekmatyar, shugaban kungiyar Hezbil Islami da ya cimma yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnatin Kabul a cikin watan jiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.