Isa ga babban shafi
Israel

Shugabannin duniya na halartar jana'izar Peres

Shugabannin kasashen duniya da dama na halartar jana’izar tsohon shugaban kasar Isra’ila Shimon Peres wadda za a yi a birnin Tel Aviv a yau jumma'a, bayan ya mutu yana da shekaru 93 a duniya yayin da aka tsaurara matakan tsaro don kare lafiyar jama'a.

Tsohon shugaban Amurka Bill Clinton a gaban akwatin gawar  Shimon Peres
Tsohon shugaban Amurka Bill Clinton a gaban akwatin gawar Shimon Peres Fuente: Reuters.
Talla

Daga cikin manyan bakin kuwa, har da Barack Obama na Amurka da Francois Hollande na Faransa, da kuma shugabannin kasashen Jamus da Poland.

Har ila yau akwai mutane kamar Yerima Charles na Ingila da kuma sarkin Spain Felipe na 6, yayin da shugaban Falasdiniwa Mahmoud Abbas ya tabbatar da cewa zai halarci jana’izar.
 

Minsitan tsaron cikin gidan Isra’ila Gilad Erdan ya ce, an baza jam’ian tsaro sama da dubu 8 musamman akan titunan da suka tashi daga ginin majalisar dokokin kasar zuwa makabartar Mont Herzl da ke birnin, in da za a binne tsohon Firaministan.
 

An dai bayyana Shimon Peres a matsayin wanda ya taka gagarumar rawa a tarihin kafuwar Isra’ila da kuma abubuwan da suka biyo baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.