Isa ga babban shafi
Syria

Rasha ta yi watsi da barazanar Amurka kan Syria

Kasar Rasha ta yi watsi da barazanar Amurka ta dakatar da tattaunawa da ita, in da ta ce, za ta ci gaba da kai hare-haren sama kan mayakan ISIS a Syria, duk da rokon da Majalisar Dinkin Duniya ke yi na ganin an tsagaita wuta don kai kayan agaji.

Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov
Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov REUTERS/Andrew Kelly
Talla

Kakakin fadar shugaban kasar Dmitry Peskov ya ce, duk da cika bakin da Amurka ke yi, suna bukatar ganin an aiwatar da yarjejeniyar hadin-kai a tsakaninsu don yin aiki tare wajen murkushe mayakan ISIS.

Sai dai jami’in ya ce, Rasha za ta ci gaba da kai hare-haren kan wadanda ta bayyana a matsayin yan ta’adda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.