Isa ga babban shafi
Saudi-Amurka

Matakin Saudiya zai iya yi wa Amurka illa

Kasar Saudi Arabia na nazari kan matakin da za ta dauka kan Amurka sakamakon amincewar da majalisar dattawan kasar ta yi na gurfanar da ita a gaban kotu don neman diyya kan 'yan uwan mutanen da suka mutu sakamakon harin ta’addancin 11 ga watan Satumba na shekarar 2011.

Shugaban Amurka Barack Obama da sarkin Salman na Saudiya a birnin Riyadh
Shugaban Amurka Barack Obama da sarkin Salman na Saudiya a birnin Riyadh Reuters
Talla

Farfesa Abdulkaliq Abdallah na jami’ar Dubai ya ce, Saudiya na iya janye biliyoyin kudin ajiyarta da kadarorinta da kuma hannayen jarin da ke Amurka, abin da zai iya durkusar da tattalin arzikin Amurkan.

Masanin ya kuma ce, Saudiya na kuma iya janyewa daga hadin-kan da take bai wa Amurka wajen yaki da ta’addanci da kuma sanya kawayenta na kasashen Larabawa su juya wa Amurkar baya.

Ministar harkokin wajen Sweden, Margot Wallstrom ta taba sukar Saudiyar wadda nan take, ta janye huldar diflomasiyya da ita, sannan kuma ta yi barazana ga harkokin cinikayyar kasar a kasashen Larabawa, matakin da ya tilsata wa Sweden neman gafara.

Tuni dai shugaba Barack Obama ya bayyana matakin da Majalisar ta dauka a matsayin babban kuskure.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.