Isa ga babban shafi
Philippines

MDD za ta binciki kashe mutane a Philippines

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, za ta gudanar da bincike kan yadda shugaban kasar Philippines Rodrigo Duterte ke kashe mutane da sunan yaki da masu amfani da miyagun kwayoyi.

Shugaban Philippines Rodrigo Duterte da ke kashe masu amfani da miyagun kwayoyi a kasar
Shugaban Philippines Rodrigo Duterte da ke kashe masu amfani da miyagun kwayoyi a kasar REUTERS/Lean Daval Jr
Talla

Shugabar yaki da cin zarafin dan Adam ta majalisar, Agnes Callamard ta ce a shirye take ta ziyarci kasar muddin za a ba ta dama da kuma kare lafiyar mutanen da take bukatar ganawa da su.

A makon jiya ne, shugaba Duterte ya ce a shirye yake ya bai wa jami’an majalisar da kungiyar kasashen Turai damar gudanar da bincike kan mutanen da aka kashe tun bayan kama aiki a matsayin shugaban kasa watanni 4 da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.