Colombia za ta kawo karshen yakin shekaru 50 a yau
Yau ne ake saran shugaban kasar Colombia Juan Manuel Santos zai sanya hannu kan yarjejeniyar kawo karshen yakin basasar kasar da shugaban kungiyar 'yan tawayen FARC, Timoleon ‘Timochenko’ Jimenez.
Wallafawa ranar:
Gwamnatin kasar ta ce, banagarorin biyu za su rattaba hannun ne da misalin karfe 5 na yamma agogon kasar a wani kasaitaccen bikin kawo karshen yakin shekaru 50.
Bikin wanda zai gudana a birnin Catargena mai dimbin tarihi, zai samu halartar sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon da sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry da kuma wasu shugabanin kasashen Latin Amurka, da suka hada da Raul Castro na Cuba wanda kasarsa ta jagoranci tattaunawar da aka kwashe shekaru 2 ana yi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu