Isa ga babban shafi
CANADA

An samu kudaden yaki da cutar Sida da Malaria

Wani asusu da aka kaddamar a Montreal na kasar Canada da zimmar tara Dalar Amurka biliyan 13 don kawar da cutar Sida da tarin fuka da Malaria a duniya nan da shekarar 2030, ya yi nasarar samun kudaden da ake nema.

An samu kudaden yaki da cutar Sida da Malaria da tarin fuka a duniya
An samu kudaden yaki da cutar Sida da Malaria da tarin fuka a duniya @RFI
Talla

Firministan Canada, Justin Trudeau ya shaida wa taron masu ruwa da tsaki na gidauniyar kawar da cutukan Sida da tarin fuka da Malaria cewa, idan batun kudaden da ake nema ne domin kai ga nasarar kawar da wadannan cutuka an yi nasarar samu.

Trudeau ya ce, biliyoyin Dalar da aka samu na  nufin cewa, za a ceci rayukan mutane miliyan 8 daga salwanta.

Mr.Trudeau ne dai ya karbi bakwancin taron, wanda ya sami halartar shugabannin kasashen duniya da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Kimoon da mutumin daya kirkiro manhajar Microsoft  wato, Bill Gates da mawakin nan na duniya, Bono da ke ta hakilon amfani da guminsa wajen kawar da fatara da cutuka a nahiyar Afrika.

Ya zuwa yanzu, wannan asusun ya kashe kudin da ya kai Dalar Amurka miliyan 30 wajen yakar wadannan cutuka uku, kuma an kashe akasarinsa ne a kasashen Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.