A yau ne Majalisar Dinkin Duniya ke fara gudanar da taronta kashi na 71 a birnin New York na Amurka, in da za ta fara tattaunawa kan matsalolin ‘yan gudun hijira da kuma bakin da ke tsallakawa nahiyar Turai. Wannan dai na zuwa ne bayan daruruwan ‘yan gudun hijira da baki sun rasa rayukansu a yunkurinsu na shiga Turai, yayin da wasunsu ke ci gaba da zama cikin kunci a kan iyakokin wasu kasashen. Akan wannan ne Abdurrahman Gambo Ahmad ya tattauna da Farfesa Habu Muhammad na sashen koyar da kimiyar siyasa a jami’ar Bayero da ke Kano a Najeriya.
Sauran kashi-kashi
-
Mukhtar Bello kan rikicin siyasar Senegal
A wannan Juma’a ake kammala yakin neman zaben shugaban Senegal, kasar da rikicin siyasa da ya auku a cikinta a baya-bayan nan ya gaza yin mummunan tasiri a kanta duk kuwa da jan hankalin duniya da lamarin ya yi.22/03/202403:40 -
Yahuza Getso kan fargabar gwamnatin Najeriya na kai hari karin wasu makarantu
Yayin da ake ciki gaba da samun karuwar satar dalibai a Najeriya, Gwamnatin kasar ta bayyana fargabarta tare da yin gargadin cewa za’a iya kaiwa wasu makarantu a jihohin kasar 14 har da babban birnin tarayya Abuja.Shin hakan ya nuna gazawar gwamnatin kasa ta fannin tsaro kenan? Abdulkadir Haladu Kiyawa, ya tattauna da Dakta Yahuza Ahmad Getso masanin tsaro a Najeriyar.12/03/202403:25 -
Sheikh Sani Yahaya Jingir kan fa'idar azumin watan Ramadan
A yayin da alummar musulmi daga kasashe da dama na duniya suka fara Azumin watan Ramadan, daya daga cikin manyan malaman addninin musulunci a Nijeriya, Sheikh Muhamad Sani Yahaya Jingir, ya yi karin haske akan irin fa'idar dake tattare da Azumin watan Ramadan ga abun da yake cewa a zantawarsu da wakilinmu na Jos Tasiu zakari.11/03/202402:58 -
Saudatu Abubakar kan bikin ranar mata ta duniya
Ranar 8 ga watan Maris din kowacce shekara, rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware don bikin ranar mata da ke da aniyar lalubo matsalolin da mata ke fuskanta da kuma duba hanyoyin warware su.08/03/202403:31 -
Umar Alangawari kan kai wa motocin dakon kayan abinci da rumbuna hari
Batun kai hari tare da daka wawa kan rumbunan ajiyar kayayyakin abinci na hukumomi a wasu yankunan Najeriya na neman zama ruwan dare, la’akari da yadda a ‘yan kwanakin nan hakan ta rika faruwa, yayin da kuma a wasu lokutan aka rika tare motocin dakon abincin tare da afka musu, lamarin da ake alakantawa da tsananin tsadar rayuwa da yunwar da ke addabar dimbin mutane a Najeriya.05/03/202403:19