Isa ga babban shafi
WHO

Zika barazana ce ga lafiyar Mata

Masu bincike kan cutar Zika a kasar Amurka sun bayyana cewar cutar na iya ci gaba da yaduwa a al’aurar mace a tsawon kwanaki idan ta kamu da cutar, wanda kuma ke iya kara yaduwarta.

Mata masu dauke da cutar Zika na haihuwar jarirai da nakasar jiki.
Mata masu dauke da cutar Zika na haihuwar jarirai da nakasar jiki. REUTERS/Denis Balibouse
Talla

Sakamakon binciken da aka wallafa a mujallar lafiya da ake kira Journal Cell a Jami’ar Yale, ya bayyana samun Karin yaduwar cutar ta hanyar jima’i.

Farfesa Akiko Iwasaki da ya jagoranci binciken ya ce sun gano yadda cutar ke bazuwa a al’auran mace bayan kwanaki 4 zuwa 5.

Yanzu haka ana ci gaba da samun karuwar kasashen da ake samu masu fama da cutar.

Masanan sun ce sabon binciken kamar gargadi ga mata baki daya.
Tuni masu bincike a Faransa suka gano cewa kwayar cutar zika ba mata masu juna biyu kawai ta ke yi wa illa ba, Cutar kan haifar da shanyewar jiki.

Mata dai masu cutar Zika na haihuwar jarirai da nakasar jiki.

Ana kamuwa da Cutar Zika ne daga cizon Sauro. Kuma har yanzu dai babu wani cikakaken rigakafin cutar.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce cutar a yanzu ta yadu zuwa kasashe 41, sai dai ta fi illa a Brazil inda mutane miliyan guda da rabi suke dauke da ita, yayin da aka haifi jarirai 641 da nakasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.