Isa ga babban shafi
Turkiya

Turkiya ta kori Janar Janar na soji 149

A ci gaba da tsauraran matakan da ta ke dauka bayan yunkurin juyin mulkin kasar, gwamnatin Turkiya ta sanar da korar Janar Janar na soji 149 tare da rufe kafofin yada labarai da dama.

Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan
Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan REUTERS/Umit Bektas
Talla

Bayanan da gwamnatin kasar ta bayar sun nuna cewar ,an salami Janar Janar na sojin kasa 87 da kuma 30 daga sojin sama da kuma wasu 32 daga sojin ruwa saboda rawar da suka taka a yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba.

Sanarwar ta kuma ce, an kori wasu manyan hafsoshi dubu 1 da 99 da matsakaita 436, yayin da aka rufe gidajen talabijin 16, na radio 23 da na jaridu 45 da mujallu 15.

Tuni dai aka kama 'yan Jaridu 42 aka tsare duk dai saboda zargin su wajen taka rawa a yunkurin juyin mulkin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.