Ana azabtar da yara a yaki da ta'addanci- HRW
Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch ta yi zargin cewa, ana ci gaba da tsare kananan yara tare da azabtar da su sakamakon matakan tsaron da jami’ai ke dauka wajen yaki da masu tsattsauran ra’ayi na kungiyar IS a Iraqi da Syria da kuma Boko Haram a Najeriya.
Wallafawa ranar:
Rahotan da kungiyar ta fitar a yau, ya nuna yadda ake ci gaba da tsare kananan yara a kasashe 6 da ke fama da tashe-tashen hankula da suka hada da Afghanistan da Jamhuriyar Demokiradiyar Congo da Iraqi da Isra'ila da yankin Falasdinu da Najeriya da kuma Syria.
Jo Becker, daraktan kare muradun yara na kungiyar Human Right Watch ya ce, gwamnatoci na tsare kananan yara na dogon lokaci ba tare da mika su a kotu ba, kuma ya ce, ana tsare da yara dubu 1 da 433 a Syria kadai, yayin da aka sake 436 daga cikin su.
Mr. Becker ya kara da cewa a Najeriya kuwa, ana tsare da yara 120 a barikin Giwa kuma wasu daga cikin su da ke da shekaru kasa da 6, sun kwashe shekaru a hannun jami'an tsaro.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu