Isa ga babban shafi
Bosnia

An tuna kisan kiyashin Srebrenica a Bosnia

Dubban jama’a ne suka hada gangami domin tunawa da jimamin kisan kiyashin da aka aikata a Srebrenica na Bosnia, shekaru 21 da su gabata a lokaci yakin da ya afkawa kasar Bosnia Herzegovina

Ana tuna Kisan musulmin Bosnia a Srebrenica
Ana tuna Kisan musulmin Bosnia a Srebrenica REUTERS/Dado Ruvic
Talla

Kisan kiyashin Srebrenica shi ne mafi muni a Nahiyar Turai bayan yakin duniya na biyu.

A cikin watan Yulin 1995, ne sojojin Sabiyawan Bosnia suka afkawa garin Srebrenica inda suka yi wa sama da musulmai dubu takwas akasarinsu maza da kananan yara kisan gilla ana saura watanni biyar da kawo karshen yakin kabilanci da ya afkawa kasar ta Bosnia Herzegovina.

A yau Litinin dubban jama’a suka halarci gangamin tuna kisan na Srebrenica.

Garin Srebrenica na ciki wani hali inda matan da aka sa su takabar dole da kuma wadanda wannan kisan kiyashi ya mayar da su marayu ke zub da hawayen abin da ya faru shekaru 21 da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.