Isa ga babban shafi
Madagascar

An kai harin taaddanci a Madagascar har mutane uku sun mutu, 92 sun jikkata

A kasar Madagascar, wani dan tatsitsin yaro na daga cikin mutane uku da suka gamu da ajalin su yayin da wani gurneti ya tashi a babban birnin kasar Anttananarivo, a wani al'amari da ake dangantashi da ayyukan ta'addanci.

Masu ayyukan agaji na taimakawa bayan harin gurneti a kasar Madagascar
Masu ayyukan agaji na taimakawa bayan harin gurneti a kasar Madagascar AFP/RIJASOLO
Talla

Bayanai na cewa an kai wannan hari ne a wani filin wasanni na Mahamasina dake birnin Antananarivo yammacin lahadi.

Mamatan na da shekaru tsakanin 16 zuwa 18.

Akwai kuma wasu mutane 91 da suka jikkata.

Shugaban kasar Henry Rajaonarimampianina wanda ya ziyarci asibiti domin gaida mutanen da suka jikkata ya danganta harin ga munin adawar siyasa .
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.