Isa ga babban shafi
Wasanni

Yau ake jana'izar Muhammad Ali a Amurka

A yau jumma’a za a yi jana’iar tsohon zakaran damben duniya Muhammad Ali a mahaifarsa da ke Louisville na jihar Kentucky ta kasar Amurka.

Marigayi Muhammad Ali
Marigayi Muhammad Ali REUTERS/Andreas Meier/File Photo
Talla

Ana saran shugabannin kasashen duniya da suka hada da shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan da sarki Abdallah na Jordan za su halarci jana’izar marigayin wanda ya bar duniya a ranar jumma’ar da ta gabata sakamakon cutar kyarmar jiki da ya yi fama da ita na tsawon shekaru fiye da 30, kuma ya rasu yana da shekaru 74 da haihuwa.

Tsohon shugaban Amurka Bill Clinton da kuma dan wasan barkwanci Billy Crystal na cikin wadanda za su gabatar da kasida a taron jana’izar.

Sai dai shugaban Amurka na yanzu Barack Obama ba zai samu damar halartar jana’izar ba duk da cewa a baya, ya yi nazarin halartar jana’izar amma hakan ya ci tura saboda bikin kammala karatu da 'yarsa ke yi a yau.

Shahararren dan wasan Hollywood Will Smith da tsohon zakaran damben duniya Lennox Lewis za su kasance cikin wadanda za su dauki akwatin gawar Muhammad Ali, yayin da dubban jama’a za su layi a kan titin da za a bi da gawar diomin isar da ita kushewa.

Za a dai binne marigayin da misalin karfe 9 agogon Amurka wanda ya yi dai dai da karfe biyu agogon Najeriya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.